logo

HAUSA

Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 7.52

2021-08-23 11:02:17 CMG

Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Afrika ya zarce miliyan 7.52_fororder_0823-Africa CDC-faiza-2

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Africa CDC, ta ce zuwa yammacin jiya Lahadi, adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a nahiyar ya kai 7,520,393.

Cibiyar ta kara da cewa, yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu a nahiyar kuma ya kai 188,654. Yayin da wasu 6,621,026 suka warke daga cutar a fadin nahiyar.

A cewa cibiyar, cutar ta fi kamari a kasashen Afrika ta Kudu da Morocco da Tunisia da kuma Habasha.

A fannin yawan wadanda suka kamu, yankin Kudancin Afrika ne ke kan gaba sai yankin arewacin nahiyar dake bi masa baya, yayin da tsakiyar nahiyar ya kasance mai mafi karancin adadin wadanda suka kamu. (Fa’iza Mustapha)

Faeza