logo

HAUSA

Gwamnatin kasar Sin tana da niyya da kwarin gwiwa wajen kiyaye wadata da zaman karko a Hong Kong

2021-03-30 20:59:31 cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata cewa, Hong Kong yankin musamman ne na kasar Sin, kuma harkokin Hong Kong harkokin cikin gida ne na kasar Sin kadai.

Kaza lika gwamnatin kasar Sin tana da niyya, da kwarin gwiwar kare ikon mulkin kasa, da tsaron kasa, da bunkasuwar kasa, da wadata da zaman karko na Hong Kong. Duk wani yunkuri na tsoma baki cikin al'amuran Hong Kong, da kuma matsa lamba ga kasar Sin ba zai yi nasara ba.

A wannan rana ne kuma aka rufe zama na 27 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 13, inda aka kada kuri’a ba tare da wata hamayya ba, don amincewa da sashe na I da na II da aka yiwa gyaran fuska, na muhimmiyar dokar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin.

Su dai wadannan sassa biyu na dokar, sun shafi batun tsarin da ake bi wajen zabar jagoran yankin, da tsarin kafa majalisar wakilan yankin, da yadda ake zaben mambobin majalisar.

Game da haka, kakakin ta bayyana cewa, matakin da zai ba da tabbaci a fannin tsare-tsare ga aiwatar da manufar 'Kasa daya amma tsari iri biyu', da tabbatar da ka'idar '’Yan kishin kasa su kula da harkokin Hong Kong', da kwanciyar hankali na dogon lokaci a yankin na Hong Kong, wanda ke nuna burin bai daya na dukkan Sinawa, ciki har da ‘yan uwa a Hong Kong. (Bilkisu)