logo

HAUSA

Demokuradiyya, Hakki Ne Na Al’ummomin Kasa Da Kasa

2021-09-23 20:42:17 CRI

“Demokuradiyya, ba wani nau’in ‘yancin mallaka ne na wata kasa ba, a’a, hakki ne na al’ummomin kasa da kasa.” Shugaba Xi Jinping ya bayyana haka cikin jawabinsa a yayin babbar muhawarar babban taron MDD karo na 76 a ranar 22 ga wata, wanda ya sa jama’a tunani sosai.

A kasar Sin, manufar demokuradiyya ita ce jama’a. Ko ta hanyar gudanar da zabe, ko ta hanyar tafiyar da tsarin jam’iyyu, dukkansu ana yinsu ne domin zabar mutanen da suka cancanci tafiyar da harkokin kasa yadda ya kamata, a kokarin kawo wa jama’ar Sin alheri. An tsai da kuduri da tsara doka kan wasu muhimman fannoni ne ta hanyar demokuradiyya daga farko zuwa karshe. Karkashin irin wannan tsarin demokuradiyya, kasar Sin ta kan nada masu basira da kwarewa a matsayin jami’ai ta hanyar yin zabe da kuma jefa kuri’a. A wani bangare, jama’a su kan zabi wakilansu a gundumomi da garuruwa ne kai tsaye ta hanyar jefa kuri’a, yayin da ake ci gaba da yin zabi a tsakanin wadannan wakilan jama’a don zabar wakilan jama’a a babban mataki. Jama’a su kan zabi wakilansu domin shiga harkokin siyasa da ba da shawara kan harkokin siyasa ta hanyar jefa kuri’a, tare da zabar shugaban kasa. Sa’an nan kuma wajibi ne a jarraba kwarewar jami’an kasar Sin a dukkan fannoni don tabbatar da cewa, suna bauta wa jama’a da zuciya daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa binciken jin ra’ayoyin jama’a da kwalejin John F. Kennedy na jami’ar Harvard ya gudanar cikin shekaru 10 a jere ya nuna cewa, sama da kaso 90 cikin 100 na jama’ar Sin sun amince da yadda JKS ke mulkin kasar Sin a kowace shekara.

Shaidu sun tabbatar da cewa, yadda kasar Sin take tafiyar da harkokin siyasa bisa demokuradiyya, ya dace da hakikanin halin da take ciki. Yadda take tafiyar da harkokin kasa bisa demokuradiyya mai salon musamman na kasar Sin ya girgiza duniya sosai. Jama’ar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4, sun fita daga kangin talauci. Sin ta ba da jagora wajen samun nasarar dakile yaduwar annobar COVID-19 a duniya, ta kuma dauki shekaru da dama tana taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Michel Aglietta, wani masanin kasar Faransa ya yi nuni da cewa, yadda kasar Sin ke kokarin kawo wa jama’arta alheri, shi ne demokuradiyya. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan