logo

HAUSA

Majalisar zaman lafiyar Ghana ta bukaci a zauna lafiya yayin dakon sakamakon shari’ar zaben kasar

2021-03-01 12:39:39 CRI

Majalisar zaman lafiyar Ghana ta bukaci a zauna lafiya yayin dakon sakamakon shari’ar zaben kasar_fororder_加纳.JPG

Majalisar zaman lafiya ta kasar Ghana ta bukaci masu ruwa da tsaki a harkar gudanar da shari’ar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar da su tabbatar da zaman lafiya a kasar yayin da ake sauraron hukuncin da kotun kolin kasar za ta yanke a ranar Alhamis.

Cikin wata sanarwar da ta fitar, majalisar zaman lafiyar Ghana ta bukaci dukkan bangarorin dake jayayya a kasar tsakanin tsohon shugaban kasar Ghanan John Dramani Mahama, da shugaban kasar mai ci Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, da hukumar zaben kasar da su mutunta sakamkon shari’ar da kotun kolin kasar za ta yanke ba tare da yin la’akari da wane ne ya yi nasara ko kuma wane ne bai yi nasara a shari’ar ba.

Ta kuma bukaci kafafen yada labarai, da masu sharhi kan al’amurran siyasa, da kuma dukkan ‘yan kasar da su yi taka tsan-tsan kan rahotanninsu da tattaunawarsu game da batutuwan dake shafar harkokin siyasar kasar kana su yi amfani da kalaman da ba za su kawo tashin hankali a kasar ba.

Majalisar ta kuma bukaci dukkan mutanen kasar Ghana da su rungumi matakan tabbatar da zaman lafiya wajen bayyana korafe korafensu cikin lumana, ko dai ta hanyar matakan shari’a ko kuma wata hanyar warware sabani cikin lumana.(Ahmad)

Ahmad