logo

HAUSA

Isra’ila za ta rufe yammacin kogin Jordan da zirin Gaza saboda zabe

2021-03-23 10:43:21 CRI

Rundunar sojojin kasar Isra’ila, ta ce za a rufe yammacin kogin Jordan da zirin Gaza tsawon kwana guda, yayin da al’ummar kasar ke fara kada kuri’un su, a zaben ‘yan majalissun dokokin kasar.

Cikin wata sanarwa, rundunar sojojin ta ce za a rufe yankunan biyu ne, tun daga tsakar daren ranar Litinin zuwa Talata, kana ana sa ran sake bude su tsakanin ranar Talata zuwa Laraba.

Yayin da yankunan biyu ke rufe, za a dakatar da zirga zirga a dukkanin mashigun Isra’ila da na yankunan Falasdinawa, in ban da wadanda suka shafi ayyukan jin kai, da na ayyukan jinya na gaggawa.

Isra’ila za ta gudanar da zaben ‘yan majalissun dokokin kasar na 4 a cikin shekaru 2 a Talatar nan.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Isra’ila ya bayyana cewa, za a sake rufe yankunan biyu, tun daga ranar 26 ga watan nan na Maris zuwa 3 ga watan Afirilu, lokacin da za a kammala bikin hutun al’ummar Yahudawa.

Da ma dai Isra’ila ta saba rufe wadannan yankuna biyu a lokutan hutu na bikin Yahudawa, bisa dalilan da take cewa na tsaro ne. (Saminu)

Saminu