logo

HAUSA

An yi zaben shugaban kasar Jamhuriyar Kongo cikin lumana

2021-03-22 11:08:40 CRI

Hukumomi a Jamhuriyar Kongo sun bayyana cewa al’ummar kasar sun gudanar da zaben shugaban kasa a jiya Lahadi cikin kwanciyar hankali da lumana.

An dan samu jinkirin bude rumfunan zabe a kasar kamar yadda aka tsara tun da farko sakamakon ruwan sama. Kimanin mutane miliyan 2.5 ne suka jefa kuri’unsu domin zaben shugaban kasa daga cikin ‘yan takara 7 da suka fafata a zaben, wanda ya hada har da shugaban kasar mai barin gado Denis Sassou Nguesso. Tun gabanin zaben an baiwa jami'an sojoji damar kada kuri'unsu wanda suka kammala ya zuwa ranar 17 ga watan Maris domin bada damar kiyaye rumfunan zaben kasar a zaben na ranar Lahadi

An katse hanyoyin sadarwar intanet a duk fadin kasar ‘yan sa’o’i kadan gabanin fara zaben, amma ba a katse hanyoyin kiran waya ko tura sakonni ba kamar yadda ya faru a shekarar 2016. Ana tsammanin samun sakamakon zaben nan da kwanaki biyu ko uku masu zuwa.

Babban abokin hamayyar shugaban kasar mai barin gado kuma dan takarar da bai yi nasara ba a zaben shugaban kasar na shekarar 2016, Guy Brice Parfait Kolelas, an kwantar da shi a asibiti kwana guda gabanin zaben bayan gwajin da aka yi masa ya nuna cewa ya kamu da cutar COVID-19. Jami’in gangamin yakin neman zabensa ya sanar cewa zai tafi zuwa kasar Faransa domin neman lafiya.

A kasar Kongo shugaban kasar da aka zaba zai shafe wa’adin shekaru biyar ne idan ya samu mafi yawan kuri’u, kuma ana gudanar da zagaye na biyu na zaben tsakanin ‘yan takara biyu mafiya yawan kuri’u idan har ba a samu dan takarar da ya samu kuri’u mafiya rinjaye a zagayen farko na zaben ba. Shugaban kasar mai barin gado Nguesso yana neman wa’adin shugabancin kasar a karo na 5 a jere tun daga shekarar 1997.(Ahmad)