logo

HAUSA

Shugaban Algeria zai rushe majalisar wakilan kasar

2021-02-19 10:52:25 CRI

Shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune, ya sanar da cewa, yana gab da rushe majalisar wakilan kasar, gabanin gudanar da zaben wuri.

A wani jawabin da aka watsa ta gidan talabijin na kasar ENTV a jiya Alhamis, shugaba Tebboune wanda ya ce zai rushe majalisar, ya ce, an sanya bukatun da aka gabatar yayin zanga-zangar da aka yi a shekarar 2019, cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha