logo

HAUSA

Shin Amurka Maras Gaskiya Za Ta Iya Jagorantar Aikin Yaki Da Annobar COVID-19 A Duniya?

2021-09-23 21:23:57 CRI

Ranar 22 ga wata bisa agogon wurin, shugaba Joe Biden na kasar Amurka ya shugabanci taron kolin duniya kan annobar COVID-19 ta kafar bidiyo, inda ya sha ambato gudummowar da Amurka ta bayar wajen yaki da annobar a duniya, tare da gabatar da shirin ba da tallafin alluran riga kafi ga kasashen duniya a mataki na gaba. Amma akasarin ra’ayoyin jama’a sun yi mamaki kan shirya taron da kuma babban shirin Amurka kan yaki da annobar.

A matsayinta na kasar da ta fi gazawa wajen yaki da annobar a duniya, ya zuwa yanzu mutane fiye da miliyan 42.5 ne suka kamu da annobar a Amurka, yayin da wasu fiye da dubu 680 suka rasu sakamakon annobar. Ga alama Amurka ba ta cancanci jagorantar aikin yaki da annobar a duniya ba. Tun bayan barkewar annobar, ‘yan siyasan Amurka sun fi sha’awar baza kwayar cutar siyasa a duniya, a maimakon ba da nasu gudummowa.

A daidai wannan lokaci ne Amurka ta yi amfani da damar shirya babban taron MDD wajen gudanar da wannan taron kolin duniya kan yaki da annobar. Kowa ya fahimci nufinta na siyasa. Wasu na ganin cewa, dalilin da ya sa Amurka ta yi haka shi ne domin dawo da martabar ta, wadda ta gaza wajen yaki da annobar, da boye kunyar da ta ji sakamakon janye sojojinta daga kasar Afghanistan cikin hanzari, da kuma yin takara da manyan kasashen duniya ta hanyar samar da alluran rigakafin annobar. Kamar yadda kafofin yada labaru na kasar Rasha suka ruwaito cewa, Biden ya gaggauta ayyana Amurka a matsayin jagorar duniya wajen yaki da annobar, amma ba za a iya bai wa Amurka irin wannan shugabanci ba. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan