logo

HAUSA

Marbatar Scott Morrison Ta Zube

2021-09-20 20:55:59 CRI

Jaridar “The Guardian” ta kasar Birtaniya, ta yi wa firaminista Scott Morrison na kasar Australiya ba’a, sakamakon kunyar da ya ji a kwanan baya. Jaridar ta ce, ana kiran mista Morrison da sunaye da dama, amma ba a taba kiransa da ‘pal’ ba. Wanda a karon farko ya kira shi “pal” shi ne shugaba Joe Biden na Amurka, wanda Morrison ke kokarin kulla abota da shi.

Kwanan baya, Australiya ta soke yarjejeniyar da ta daddale da kasar Faransa, kan sayen jiragen ruwan karkashin ruwa da dama, inda ta hada kai da Amurka da Birtaniya, tare kuma da kafa sabon kawancen tsaro.

A yayin taron manema labaru da Amurka, Birtaniya da Australiya suka shirya cikin hadin gwiwa, dangane da kafa sabon kawancen tsaron a kwanan baya, Biden ya manta sunan Morrison yayin da yake gode masa ta kafar bidiyo, inda ya kira shi “pal”, yayin da Morrison ya rika dariya tare da jinjinawa.

Kila Morrison mutum ne mai hakuri, ba ya tsoron martabarsa ta zube a bainal jama’a. Amma a matsayinsa na firaministan Australiya, Morrison yana yin caca da makomar kasarsa ta Australiya. Da farko Amurka, Birtaniya da Australiya, sun daddale yarjejeniya game da cinikin jiragen ruwa karkashin ruwa ne, bayan da Australiya ta ci amanar Faransa. Inda da kyar Faransa ta dakatar da fushinta. Baya ga biyan makudan kudaden diyya, kila Australiya za ta fuskanci martanin Faransa. Na biyu kuma, Australiya ta soke yarjejeniya da Faransa, lamarin da zai yi illa cikin dogon lokaci, ta fuskar harkokin diplomasiyya da tattalin arziki. Shin wa zai hada kai da irin wannan kasa maras gaskiya? (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan