Amurka ta fara korar dimbin bakin da suka shiga Amurka ba tare da izini ba
2021-09-21 15:14:22 CRI
Kwanan baya, baki fiye da dubu 10 sun shiga kasar Amurka ta hanyar ketare kogin da ke bakin iyakar kasashen Mexico da Amurka, daga bisani sun kafa sansani a wata babbar gada a birninDel Rio a jihar Texas. Kafofin yada labaru na Amurka sun ruwaito a ranar 19 ga wata cewa, hukumomin aiwatar da dokar Amurka sun fara korar wadannan baki masu dimbin yawa.
Labarai Masu Nasaba