logo

HAUSA

Sin na adawa da sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Habasha

2021-09-22 19:25:48 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa Larabar nan cewa, kasarsa tana adawa da sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa kasar Habasha.

A kwanakin nan ne, shugaban Amurka Joe Biden, ya ba da umarnin shugaba inda ya bayar da iznin kakaba sabon takunkumi kan kasar Habasha, dangane da rikicin dake faruwa a cikin kasar.

Zhao ya jaddada cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana ba da shawarar cewa, ya kamata musaya tsakanin kasashe ya dace da dokoki da ka’idojin mu’amular kasa da kasa, tana kuma adawa da amfani da takunkumi ko barazana don sanya takunkumi da matsin lamba, da yin katsalanda a cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe.

A don haka ya kamata Amurka ta yi taka tsan-tsan kan batutuwan da suka shafi Habasha, tare da taka rawar gani wajen mai do da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Habasha.(Ibrahim)

Ibrahim