logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi maraba da tsagaita bude wuta a yankin Tigray na Habasha

2021-06-29 19:30:09 CRI

Kasar Sin ta yi maraba da tsagaita bude wuta a yankin Tigray na Habasha_fororder_汪文斌

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya shaida wa taron manema labaran da aka saba shiryawa Talatar nan cewa, kasarsa ta yi maraba da yadda aka tsagaita bude wuta a yankin Tigray na kasar Habasha mai fama da tashin hankali, tana kuma goyon bayan dukkan bangarori a kasar, da su cimma sasantawa ta hanyar tattaunawa.

Wang ya ce, “Mun yi imanin cewa, suna da basira da karfin daidaita harkokin cikin gidan kasarsu yadda ya kamata.”

Ranar Litinin da dare ne, gwamnatin kasar Habasha ta sanar da tsagaita bude wuta a yankin na Tigray dake arewacin kasar da rikici ya shafa, biyo bayan bukatar gwamnatin rikon kwarya ta jihar. Manufar tsagaita bude wutar dai, ita ce samun damar kai taimakon jin kai zuwa yankin, da ma gudanar da ayyukan gona, yayin da lokacin damuna ke karatowa.(Ibrahim)

Ibrahim