logo

HAUSA

Yara 100 na daga cikin mutane 200 da aka kashe a sansanin ‘yan gudun hijira a Habasha

2021-08-10 10:33:36 cri

Yara 100 na daga cikin mutane 200 da aka kashe a sansanin ‘yan gudun hijira a Habasha

Shugabar asusun kula da kananan yara na MDD, Henrietta Fore, ta bayyana kaduwa game da rahoton kisan sama da ‘yan gudun hijira 200, ciki har da yara 100 a Habasha.

A ranar Alhamis ne aka kai hari kan iyalai ‘yan gudun hijira dake samun mafaka a wata cibiyar kiwon lafiya da wata makaranta.

A cewar Henrietta Fore, rikici a baya-bayan nan ya tilasta raba mutane sama da 100,000 da matsugunansu, tana mai cewa, yanzu haka mutane miliyan 2 ne suka rasa mahallansu. UNICEF ya yi kiyasin adadin yaran da za su yi fama da tamowa mai tsanani cikin watanni 12 masu zuwa a Tigray, zai ninka na yanzu har sau 10.

Rabin mutanen da shirin samar da abinci na MDD WEP ya tsara kai wa dauki kadai ya tallafawa, cikinsu akwai al’ummomin yankin arewacin Habasha dake gab da shiga matsalar yunwa. Baya ga haka, shirin na fuskantar karancin abinci da kudi da man fetur da kayayyakin sadarwa. (Fa’iza Mustapha)