Jami’in MDD ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yankin Tigray
2021-07-04 16:26:07 CMG
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa game da halin da ake ciki a yankin Tigray na kasar Habasha.
Ya ce, abu mafi matukar muhimmanci shi ne a tabbatar da hakikanin tsakaita bude wuta domin share fagen shiga tattaunawa don warware rikicin siyasar yankin Tigray.
Babban sakataren ya jaddada cewa, cigaba da zaman dakarun tsaron kasashen waje a yankin yana kara ruruta wutar rikicin yankin.
A hannu guda kuma, ya ce dole a samar da cikakkiyar damar kaiwa tallafi zuwa yankin, kuma ya kamata a kawar da dukkan shingayen dake hana damar shigar da kayayyakin tallafi zuwa yankin. Kuma yadda ake lalata kayayyakin more rayuwar fararen hula ba za a taba laminta ba, inji jami’in MDDr.
A cewar wasu rahotannin kafafen yada labarai, akwai kamfar abinci da makamashi a fadin birnin na Tigray, kusan mutane 400,000 sun fada cikin halin matsananciyar yunwa, kana akwai wasu mutanen kusan miliyan 2 dake daf da fadawa cikin halin yunwar, inda ake kara yin kira da samar da damammakin shigar da kayan tallafawa rayuwar bil adama zuwa yankin.(Ahmad)