logo

HAUSA

Jirgin kasan Habasha zuwa Djibouti ya yi jigilar hajoji ton miliyan 3.45 cikin shekaru 3

2021-06-19 16:12:15 CMG

Jirgin kasan Habasha zuwa Djibouti ya yi jigilar hajoji ton miliyan 3.45 cikin shekaru 3_fororder_0619-railway-Ahmad

Layin jirgin kasan da kasar Sin ta gina mai tazarar kilomita 752.7 tsakanin Habasha zuwa Djibouti ya ba da damar jigilar kayayyaki da suka kai ton miliyan 3.45 na shigi da fici a cikin shekaru uku da suka gabata, kafar yada labarai ta Fana FBC, dake yankin ta ba da rahoton a ranar Juma’a.

Jigin kasan na Habasha zuwa Djibouti mai aikin da lantarki, wanda ya hade yankunan kan tudu na Habasha zuwa tashar ruwan Djibouti, yana cigaba da kara inganta ayyukansa daga kashi 25 zuwa kashi 30 bisa 100 a duk shekara tun bayan da ya fara aiki, a cewar rahoton.

A cewar babban daraktan dake kula da kamfanin jirgin kasan na EDR, Tilahun Serka, kimanin ton 800,000 na kayayyaki jirgin ya yi jigilarsu a shekarar farko da ya fara aiki, inda kuma ya kara ayyukansa zuwa ton miliyan 1.2 da kuma ton miliyan 1.45 a shekaru biyun dake biye.

Jirgin kasan ya yi nasarar jigilar kayayyakin da suka hada da manyan injina, motoci, takin zamani, da kayayyakin masarufi wadanda kamfanonin ‘yan kasuwa da kamfanonin masu hidimar fiton kayayaki ta ruwa suka shigo da su.(Ahmad)

Ahmad