logo

HAUSA

Gwamnatin Sudan ta tabbatar da komai na karkashin ikonta bayan wani yunkurin juyin mulki a kasar

2021-09-21 20:08:37 CRI

Gwamnatin Sudan ta tabbatar da cewa, ita ke rike da iko kan yanayin tsaro a birnin Khartoum, bayan ta bankado wani yunkurin juyin mulki.

Kakakin gwamnatin Sudan, kuma ministan labaran kasar Hamza Baloul Al-Amir ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, da safiyar yau Talata, aka bankado yunkurin wani rukunin sojojin tsohuwar gwamnatin kasar na juyin mulki, kuma tuni aka katse hanzarinsu.

Ministan ya kuma sanar da kame shugabannin da suka yi yunkurin, yana mai cewa, yanzu haka ana gudanar da bincike bayan dakile yunkuri na karshe a sansanin sojojin dake yankin Alshara. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha