logo

HAUSA

Sudan da Chadi za su yi hadin gwiwa don yakar ta’addanci da tsaron iyakokinsu

2021-08-30 10:15:07 CRI

Kasashen Sudan da Chadi sun jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu domin tinkarar kalubalolin ta’addanci da masu tsattsauran ra’ayi dake damunsu gami da hadin gwiwa don tsaron iyakokinsu.

Bangarorin biyu sun gudanar da taron tattaunawa na hadin gwiwa a ranar Lahadi a fadar shugaban kasa dake Khartoum, wanda shugaban majalisar mulkin kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, da shugaban gwamnatin soji na rikon kwaryar kasar Chadi Mahamat Idriss Deby Itno, suka jagoranta.

A watan Mayun shekarar 2018, kasashen Libya, Chadi, Nijer da Sudan, suka rattaba hannu kan yarjejejniyar kafa rundunar tsaron hadin gwiwa da nufin gudanar da ayyukan tsaron kan iyakokinsu domin kawar da ayyukan bata gari da kuma dakile kwararar bakin haure ba bisa ka’ida ba. (Ahmad)