logo

HAUSA

Jami’ar MDD: Karancin abinci ya kai matsayin koli a Sudan ta kudu tun bayan samun ’yancin kasar

2021-09-16 10:51:13 CRI

Jami’ar MDD: Karancin abinci ya kai matsayin koli a Sudan ta kudu tun bayan samun ’yancin kasar_fororder_0916-south sudan-Ahmad

Wata jami’ar MDD ta ce, a halin yanzu al’ummar Sudan ta kudu suna fuskantar matsalar karancin abinci mafi tsanani wanda ba su taba ganin irinta ba tun bayan samun ’yancin kan kasar daga kasar Sudan yau shekaru 10 da suka gabata.

Sama da kashi 60% na yawan mutanen kasar da aka kiyasta su miliyan 12.78 suna fama da matsanancin karancin abinci, a cewar Reena Ghelani, daraktar gudanarwa da ba da tallafi ta ofishin gudanar da ayyukan jin kai na MDD. (Ahmad Fagam)