logo

HAUSA

Ministan lafiyar Sudan ya kamu da COVID-19

2021-09-05 16:41:07 CMG

Ministan lafiyar Sudan ya kamu da COVID-19_fororder_0905-sudan-Ahmad

Gwajin da aka yiwa ministan lafiyar kasar Sudan, Omer Al-Najeeb ya nuna cewa ya kamu da cutar COVID-19.

Al-Najeeb ya sanar cewa, tun a farkon wannan makon, ya fara jin alamomin kamuwa da cutar ta COVID-19. Don haka sai aka yi masa gwajin inda sakamakon ya nuna cewa ya harbu da cutar.

Ya ce a yanzu haka yana aiki ne daga gida inda ya killace kansa, amma ya bayyana cewa yana murmurewa a halin yanzu, sakamakon riga-kafin da aka yi masa a lokacin da ya gabata.

Ministan ya bukaci jama’ar kasar da su hanzarta karbar alluran riga-kafin COVID-19 domin kare kansu da kuma iyalansu.

Kawo yanzu, Sudan tana da jimillar mutane 37,715 da aka tabbatar sun kamu da COVID-19, yayin da cutar ta kashe mutane 2,837, kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar.(Ahmad)

Ahmad