logo

HAUSA

Firaministan Sudan ya jaddada aniyar daukar matakan hana tabarbarewar al’amurra a Habasha

2021-08-16 10:40:12 CRI

Firaministan Sudan ya jaddada aniyar daukar matakan hana tabarbarewar al’amurra a Habasha_fororder_0816-Sudan-Ahmad2

Firaministan kasar Sudan Abdalla Hamdok, ya jaddada aniyar kasarsa wajen yin aiki tukuru domin yin kandagarkin hana tabarbarewar yanayin da ake ciki a kasar Habasha.

A taron manem labarai da aka shirya a Khartoum, babban birnin kasar, Hamdok ya ce, ba za su zura ido suna kallon abin da ke faruwa a makwabciyar kasarsu Habasha ba. Ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen taimakawa Habasha don dinke dukkan baraka, da samun zaman lafiya da tsaro.

Hamdok ya kara da cewa, karkashin kungiyar raya ci gaban shiyyar gabashin Afrika (IGAD), yana tuntubar shugabannin IGAD, da shiyyoyi da kuma kasashen duniya domin lalibo bakin zaren warware rikin yankin Tigray na kasar Habashan.

Ya bayyana mataki na baya bayan nan da kasarsa ta dauka na janye jakadanta dake kasar Habasha a matsayin tsari na diflomasiyya a bisa al’ada, inda ya bayyana cewa, tuni jakadan na Sudan ya riga ya koma Addis Ababa don ci gaba da gudanar da ayyukansa. (Ahmad)