logo

HAUSA

Faransa ta maida martani ta hanyar kirawo jakadunta dake kasashen Amurka da Australiya

2021-09-18 21:53:16 CRI

Faransa ta maida martani ta hanyar kirawo jakadunta dake kasashen Amurka da Australiya_fororder_A

Da yammacin jiya Jumma’a ne, kasar Faransa ta sanar da wani kudurin da ba safai a kan ga irinsa ba, wato kirawo jakadunta dake kasashen Amurka da Australiya, al’amarin da ya zama karo na farko da Faransa ta kira jakadunta dake wadannan kasashe biyu a tarihi. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya bayyana cewa, kudurin da kasarsa ta yi, shi ne martanin da ta mayar bisa bukatar shugaban kasar, ga wani abu mai tsanani da kasashen Amurka da Australiya suka yi.

Wannan abu shi ne, Amurka da Birtaniya da Australiya sun sanar a ranar 15 ga wata cewa, sun kafa wani sabon kawancen tsaro, sa’annan Australiya ta dakatar da yarjejeniyar sayen jiragen karkashin ruwa mai kunshe da zunzurutun kudade da ta daddale tare da Faransa, ta kuma karkata hankalinta kan hada gwiwa da Amurka.

Faransa ta maida martani ta hanyar kirawo jakadunta dake kasashen Amurka da Australiya_fororder_B

Takaicin Faransa ba abu ne mai ban mamaki ba. Hada baki da aka yi tsakanin kasashen Amurka da Australiya, tamkar wuka ce mai kaifi da aka daba wa Faransa. Kuma illa mafi muni ita ce illar moriyar tattalin arziki. Kafar CNN ta Amurka ta yi sharhin cewa, Faransa babbar kasa ce dake fitar da makamai zuwa duk duniya, amma yanzu Australiya ta soke yarjejeniyar da ta daddale da ita, abun da zai kawo hasarar dimbin kudade ga hukumomin tsaron gidan Faransa.

Abu na daban da ya fi yiwa Faransa radadi a jiki shi ne, yadda Amurka ta yaudare ta. Bayan da Joe Biden ya zama shugaban Amurka, gwamnatinsa ta sha nanata cewa, wai za ta yi kokarin gyara dangantakarta da nahiyar Turai, amma abun da ta yi a zahirance, ya bakantawa kasashen nahiyar rai sosai.

Ga ita Amurka, babu kasashe kawaye na ainihi, sai dai moriya ta har abada. Ya dace kasashen Turai su dauki mataki cikin ‘yanci kuma bisa radin kansu. (Murtala Zhang)