logo

HAUSA

Dangin Mutanen Da Suka Rasu A Harin Amurka: Neman Gafara Ba Zai Wadatar Ba

2021-09-19 17:36:00 CRI

Dangin Mutanen Da Suka Rasu A Harin Amurka: Neman Gafara Ba Zai Wadatar Ba_fororder_01

Dangin Mutanen Da Suka Rasu A Harin Amurka: Neman Gafara Ba Zai Wadatar Ba_fororder_02

Dangin Mutanen Da Suka Rasu A Harin Amurka: Neman Gafara Ba Zai Wadatar Ba_fororder_03

Dangin Mutanen Da Suka Rasu A Harin Amurka: Neman Gafara Ba Zai Wadatar Ba_fororder_04

A ranar 17 ga wata, Kenneth McKenzie, kwamandan hedkwatar rundunar sojan kasar Amurka ya amince cewa, jiragen sama marasa matuki na sojojin Amurka ba su kai hari kan ‘yan ta’adda a kasar Afghanistan a ranar 28 ga watan Agusta ba, a maimakon hakan, fararen hula 10 ciki har da kananan yara 7 ne suka rasa rayukansu a harin. McKenzie ya nuna bakin cikinsa kan lamarin tare da neman gafara, ya kara da cewa, zai sauke nauyin daka bisa wuyansa.

A ranar 18 ga wata da safe, wakilin CMG a birnin Kabul ya ziyarci wadanda aka kai musu hari, inda ya samu damar zantawa da Romal Ahmadi, kani ne ga Zamali Ahmadi wanda rundunar sojan Amurka ta mayar da shi a matsayin dan ta’adda.

A baya, wakilinmu ya taba zantawa da Romal Ahmadi. A wannan karo, Romal Ahmadi ya ce, kanensa da da ‘ya’yan kanensa maza 3 dukkansu sun mutu a harin, yayin da mai gidan kanensa da diyarsa suke cikin bakin ciki ya zuwa yanzu. Kafin abkuwar harin, kanensa Zamali Ahmadi ya koma gida cikin mota, tare da sanya wata babbar gangar ruwa a kan motar, wadda sojan Amurka suka mayar da ita kamar wata gangar nakiya. Sojan Amurka sun tsai da kudurin kai harin ne ba tare da yin tunani sosai ba, sun kashe fararen hula 10.

Masood, dan dan uwan Zamali Ahmadi ya yi fushi sosai ya gaya wa wakilinmu cewa, ba za a yafe wa duk wanda ya aikata wannan mugun laifi ba, tilas ne a gurfanar dasu a gaban kotu, musamman ma kasar Amurka, wadda ke yin shelar kiyaye hakkin dan Adam, amma ta kashe mutane ta hanyar kimayya da fasaha ta zamani. Lalle ta aikata laifi. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan