logo

HAUSA

An Bude Bikin Fina-finai Na Kasa Da Kasa Na Beijing Karo Na 11

2021-09-21 16:26:49 CRI

A yau Talata ne aka bude bikin fina-finai na kasa da kasa na Beijing karo na 11, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar ta shirya, yayin da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da gwamnatin birnin Beijing suka karbi bakuncinsa.

Jimillar fina-finai 889 daga kasashe da yankuna 77 ne suka shiga takarar neman lambar yabo ta Tiantan. Fina-finai 15 na fadin duniya, ciki har da “All About My Mother” na kasar Sin da “Diary of a Siege” daga kasar Rasha da “The Oath” na kasar Denmark ne aka zaba.

A karon farko, an fadada bangaren tantance fina-finan zuwa yankin Beijing da Tianjin da Hebei. Gidajen nuna fina-finai 31 sun nuna fina-finan kasar Sin da na kasashen waje kusan 300. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha