logo

HAUSA

A Karon Farko CMG Zai Watsa Shagalin Murnar Bikin Tsakiyar Yanayin Kaka Na Kasar Sin Zuwa Ketare

2021-09-19 20:57:07 CRI

Ana sa ran da misalin karfe 8 na yammacin ranar 21 ga wata babban rukunin gidan radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, zai watsa shagalin murnar bikin tsakiyar yanayin kaka na kasar Sin na shekarar 2021. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan shi ne karon farko da CMG zai a watsa shagalin a kasashen ketare.

Domin baiwa ‘yan kallo daga kasashen ketare damar kara fahimtar kyawawan al’adun Sinawa, a karon farko, kamfanin CCTV News Content zai hada gwiwa da gidajen talabijin na kasashen ketare don watsa shagalin murnar bikin tsakiyar yanayin kaka a bana. Gidan talabijin na Sinovison dake Amurka, da kamfanin Xinflix Media na Kanada, da gidan talabijin na Switch TV na Kenya, da gidan talabijin na CATV na hadaddiyar daular Larabawa, da kamfanin Enjoy TV na Malaysia da sauran kafafen yada labarai na kasashen ketare, gami da kamfanin Telediffusion na Macao da na Macau cable TV duka za su watsa shagalin.

Da zummar ba da dama ga ‘yan kallo daga ketare, domin su kara fahimtar bikin tsakiyar yanayin kaka na Sinawa, a karon farko za a watsa shagalin tare da yi bayani cikin harshen Turanci, dangane da al’adun Sinawa na murnar bikin tsakiyar yanayin kaka gami da taken shagalin da dai sauransu a bana.(Ahmad)

Ahmad