logo

HAUSA

An Kaddamar Da Harkokin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin Kan Intanet

2021-02-04 19:26:58 CRI

Yau Alhamis 4 ga wata ne aka kaddamar da harkokin murnar bikin Bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ta kafar yanar gizo ko Intanet a nan birnin Beijing. Ministan al’adu da aikin yawon shakatawa na kasar Sin Hu Heping, da shugaban babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG Shen Haixiong, sun ba da nasu jawabai ta kafar bidiyo don kaddamar da harkokin.

Wadannan harkoki sun hada da masu halin musamman na bikin Bazara, wadanda suka shafi al’adun kasar Sin, da harkokin kara fahimtar al’adu da aikin bude ido, da wasanni masu kayatarwa, da masu fasaha na gida da wajen kasar Sin za su nuna, ta yadda ’yan kallo daga sassa daban daban na duniya za su kara fahimtar bikin Bazara, duk da suna cikin gidajensu. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan