logo

HAUSA

An hallaka sama da fararen hula 132 a arewacin Burkina Faso

2021-06-06 16:33:41 CRI

Sama da fararen hula 132 aka kashe, kana an raunata fiye da 40 a hare-haren da ‘yan ta’adda suka kaddamar cikin dare a wani kauyen da ke lardin Yagha a arewacin Burkina Faso, kamar yadda Ousseini Tamboura, kakakin gwamnatin kasar ya bayyana.

‘Yan ta’addan sun afkawa kauyen Solhan dake lardin Yagha, inda suka kashe mazauna kauyen, kana sun kone gidaje da kasuwa, kamfanin dillancin labaran AIB na kasar ne ya bayyana hakan.

Kila adadin mutanen da suka mutu zai ci gaba da karuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AIB mallakin gwamnatin kasar ya bayyana. Sanarwar ta kara da cewa, tuni dakarun tsaron kasar suka kaddamar da ayyukan bincike domin gano mutanen dake da hannu wajen shirya harin.

Kawo yanzu, babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.

Bayan faruwar lamarin, shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ya ayyana makokin kwanaki uku a duk fadin kasar domin nuna juyayin   mutuwar, makokin ya fara daga ranar Asabar zuwa Litinin.

A wata sanarwar da kakakin sakataren MDD Stephane Dujarric ya fitar, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana takaicinsa bisa kashe-kashen fararen hular, kana ya bayyana bukatar gaggawa ga kasashe mambobin MDD da su kara kokari wajen taimakawa yaki da ayyukan masu tsattsauran ra’ayi kuma ba za a taba lamintar aikata muggan laifuka ba. (Ahmad)

Ahmad