logo

HAUSA

Kimanin fararen hula 100 aka kashe a arewacin Burkina Faso

2021-06-05 20:41:52 CRI

Kimanin fararen hula 100 ‘yan ta’adda suka kashe a daren jiya, a wani kauye dake arewacin Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labarai na AIB ya ruwaito cewa, ‘yan ta’adda sun kai hari wasu yankuna da dama inda suka yi harbin kan mai uwa da wabi, tare da kona wata kasuwa. Jami’ai a kasar sun bayyana yuwuwar samun karuwar adadin wadanda aka kashe.

Shugaban kasar, Roch Marc Christian Kabore, ya bada umarnin zaman makoki a kasar na sa’o’i 72, daga yau 5 ga wata zuwa ranar Litinin, 7 ga wata. (Fa’iza Mustapha)