logo

HAUSA

Sin da Burkina faso na fatan sanya hannu kan shawarar ziri daya da hanya daya

2021-06-11 11:29:12 CMG

Sin da Burkina faso na fatan sanya hannu kan shawarar ziri daya da hanya daya_fororder_王毅-wangyi-2

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, yana fatan kasarsa da Burkina Faso, za su sanya hannu kan muhimman takardu da suka shafi shawarar ziri daya da hanya daya, nan ba da dadewa ba, tare da karfafa hadin gwiwa a fannonin kiwon lafiya da kayayyakin more rayuwa.

Wang ya bayyana haka ne, yayin zantawa da takwaransa na Burkina Faso Alpha Barry ta wayar tarho. Yana mai cewa, sanya hannu kan irin wadannan muhimman takardu, zai kara kaimi tare da samar da sabbin zarafi ga kasashen biyu wajen zurfafa alaka a tsakaninsu.

A nasa bangare Barry, ya godewa kasar Sin, saboda goyon baya mai karfi da take baiwa wajen bunkasa tattalin arziki da jin dadin jama’a, musamman a yakin da take yi da COVID-19.

Ya bayyana cewa, kasar Sin tana cika alkawuran da ta yi a alakarta da Burkina Faso, lamarin da ya haifar da kyakkyawan sakamako. Ya ce kasashen biyu sun kuma ciyar da alakarsu mai makomar bai daya zuwa gaba.

Barry ya bayyana kudirin kasarsa, na zurfafa alaka da kasar Sin a fannin gina shawarar ziri daya da hanya daya, da ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon mataki.(Ibrahim)

Ibrhaim