logo

HAUSA

An kashe mutane 9 a harin Burkina Faso

2021-05-17 15:58:34 CRI

An kashe mutane 9 a harin Burkina Faso_fororder_布基纳法索

A kalla mutane 9 aka kashe a wani harin da aka kai ga jami’an tsaro na sa kai wato (VDP) a Burkina Faso a ranar Lahadi a shiyyar tsakiyar kasar, wata majiyar yankin ce ta bayyana.

Wani jami’in dan sandan yankin da ya nemi a sakaye sunansa ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu gungun mahara da ba a san ko su wanene ba sun kaddamar da harin a kan jami’an tsaron sa kai na VDP dake kauyen Palsegue, da farko adadin mutanen da aka bayyana sun mutu ya kai 9.

Sai dai kuma, hukumar gudanarwar yankin ta ce fararen hula takwas, ciki har da shugaban kauyen aka kashe a harin.

Jami’an VDP suna aikin sa kai don taimakawa dakarun tsaron gwamnatin Burkina Faso wajen shimfida zaman lafiya a kasar ta yammacin Afrika.

Tun a shekarar 2015, Burkina Faso ke fuskantar tabarbarewar al’amurran tsaro inda hare haren ta’addanci suka yi sanadiyyar rayukan sama da mutane 1,000, tare kuma da raba wasu mutanen sama da miliyan daya daga muhallansu.(Ahmad)