logo

HAUSA

Xi ya aike da sakon ta’aziyya bisa mutuwar tsohon shugaban Algeria Bouteflika

2021-09-20 20:39:11 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, a yau Litinin ya aike da sakon ta’aziyya ga shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune bisa rasuwar tsohon shugaban kasar Algerian Abdelaziz Bouteflika.

Cikin sakon nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa, marigayi Bouteflika sanannen dan kishin kasa ne kuma jagoran juyin juya halin tabbatar da samun ‘yancin kan kasar Algeria, da yankin Larabawa da kuma Afrika, sannan ya bayar da gagarumar gudummawa wajen maido da kujarar wakilin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a MDD.

A lokacin shugabancinsa, Bouteflika ya yi iyakar bakin kokarinsa wajen karfafa huldar dake tsakanin Sin da Algeria, da zurfafa hadin gwiwar kasashen da kuma kyautata alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin tana martaba dadaddiyar alakar abota dake tsakaninta da kasar Algeria, kuma a shirye take ta yi aiki tare da gwamnatin kasar Algeria da al’ummar kasar wajen kara zurfafa zumuncin dake tsakanin kasashen daga dukkan fannoni, kana za ta ci gaba da daga matsayin muhimmiyar huldar dake tsakanin Sin da Algeria.(Ahmad)

Ahmad