logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya aika da sakon jaje ga takwaransa na Algeria kan mummunar gobarar gandun daji

2021-08-17 16:27:47 CRI

Yau Talata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aika da sakon jaje ga takwaransa na kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune kan dimbin asarar rayukan mutane da jikkatar wasu cikin mummunar gobarar gandun daji a kasar.

A cikin sakon, a madadin gwamnatin Sin da jama’ar kasar, shugaba Xi ya yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu cikin gobarar, tare da jajantawa wadanda suka jikkata.

A wannan rana kuma, Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar shi ma ya aika da sakon jaje ga takwaransa na Algeria Ramtane Lamamra kan babbar gobarar. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan