logo

HAUSA

Algeria za ta fara bada riga kafin COVID-19 a watan Junairun badi

2020-12-21 13:47:34 CRI

Shugaban kasar Algeria, Abdelmajid Tebboune, ya ce kasarsa za ta fara bada alluran riga kafin COVID-19 a watan Junairun 2021.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaba Tebboune ya ce ya umarci Firaministan kasar ya gudanar da taro da kwamitin masana kimiyya dake da alhakin bibiyar yanayin annobar, domin zabo riga kafi mafi kyau, gabanin fara amfani da shi a watan Junairun 2021.

A makon da ya gabata ne, ministan lafiya na kasar Abderrahmane Benbouzid, ya shaidawa manema labarai cewa, za a bada riga kafin kyauta ga al’ummar kasar.

Kakakin kwamitin masana kimiyyar, Djamel Fourar, ya sanar a jiya cewa, cikin sa’o’i 24, an samu sabbin mutane 422 da suka kamu da cutar, mutane 391 kuma sun warke, yayin da ta yi ajalin mutane 7.

Jimilar wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar a Algeria ya kai 95,203, adadin wadanda suka mutu kuma ya tsaya kan 2,666 yayin da aka sallami 63,260 daga asibiti bayan sun warke. (Fa’iza Mustapha)