logo

HAUSA

Algeria ta yi jana’izar tsohon shugaban kasar Bouteflika

2021-09-20 16:31:42 CRI

Jiya Lahadi kasar Algeria ta gudanar da jana’izar tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, a babban birin kasar Algiers, wanda ya rasu a daren Juma’ar da ta gabata yana da shekaru 84 a duniya.

Bouteflika, wanda aka binne shi da yammacin ranar Lahadi a makabartar El-Alia inda aka binne tsoffin shugabannin kasar da dama.

A ranar Asabar shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya bayar da umarnin a sauko da tutocin kasa kasa a duk fadin kasar har na tsawon kwanaki uku domin girmama marigayi Bouteflika.

Kasar Sin ta bayyana alhinin mutuwar tsohon shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika, kamar yadda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana a ranar Lahadi. A lokacin wa’adin mulkinsa na shugabancin kasar Algeria, Bouteflika ya yi matukar karfafa huldar dake tsakanin kasar Sin da Algeria, da zurfafa hadin gwiwar abota a tsakanin kasashen, kana da karfafa zumuncin dake tsakanin al’ummun kasashen biyu, a cewar sanarwar da Zhao Lijian ya fitar.(Ahmad)

Ahmad