logo

HAUSA

Sin na goyon bayan hanyar da kasar Rasha ta zaba

2021-09-20 20:41:25 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin za ta ci gaba da mara baya ga hanyar ci gaba da kasar Rasha ta zaba da kan ta, bayan da jam’iyyar kasar mai mulki ta lashe mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ‘yan majalisar dokoki.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a Litinin din nan, Zhao Lijian ya ce zaben ‘yan majalissar dokokin Rasha, muhimmnin jigo ne a tsarin siyasar kasar, kuma sakamakon da aka fitar ya nuna alkiblar al’ummar kasar.

Kakakin ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da mara baya ga Rasha, ta yadda kasar za ta samu sabuwar nasara, karkashin jagorancin shugaba Vladimir Putin, har ta kai ga cimma burin ta na ci gaba da wadata.  (Saminu)

Saminu