logo

HAUSA

Putin: Siyasantar Da Binciken Asalin COVID-19 Ba Madogara Ba Ce

2021-09-04 16:53:37 CRI

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ce, siyasantar da batun neman asalin kwayar cutar COVID-19 ba zai haifar da komai ba ila sakamoko na rashin gaskiya.

Vladimir Putin ya bayyana haka ne jiya, a yayin zaman taron raya tattalin arzikin yankin gabashin Asiya karo na 6.

Shugaban na Rasha ya ce, wadanda suka zabi siyasantar da batun na tafka gagarumin kuskure ga aikin yaki da annobar.

A cewarsa, idan batun siyasa ya shigo, to zai rage kwarin gwiwar da ake da shi kan sakamakon da za a samar.

Ya ci gaba da cewa, dole ne binciken asalin kwayar cutar ya kasance bisa hujjoji na hakika, yana mai cewa, babu abun da siyasantar da batun zai yi face nisanta duniya daga gaskiya.

Ya kara da cewa, yana da muhimmanci a yi watsi da siyasantar da batun don a hada kai wajen yaki da annobar da tasirinta.

An kaddamar da taron karo na 6 ne a ranar Alhamis, inda za a kammala yau Asabar a birnin Vladivostok na Rasha. Taken taron na bana shi ne, “Damarmakin da yankin gabas mai nisa ke da shi yayin da duniya ke fuskantar sauyi”. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha