logo

HAUSA

Sin ta zargi Amurka da ficewa daga yarjejeniyar nan ta halasta shawagin jiragen saman kasashen juna

2021-06-08 20:19:44 CRI

A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, Rasha ta fice daga yarjejeniyar nan ta halasta shawagin jiragen saman kasashen juna ne, saboda ficewar da Amurka ta fara yi daga yarjejeniyar, duk kuwa da rashin amincewar da sassan kasa da kasa suka nuna ga hakan.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, inda ya ce matakin Amurka ya lahanta amincin da ake samu tsakanin kasashe ta fuskar ayyukan soji, da yin komai a bude tsakanin kasashen da yarjejeniyar ta shafa.

Zhao ya kara da cewa, Rasha ta yi yunkurin ganin yarjejeniyar ba ta rushe ba, sai dai kuma ba ta samu wani goyon baya da ya kamata daga tsagin Amurka da wasu karin kasashen ba.

Jami’in ya ce a zahiri take cewa, ana iya cimma makoma mai haske ne kawai, ta hanyar tattaunawa da hadin gwiwa, a maimakon ware kai. Kaza lika Sin na kira ga Amurka, da ta saurari damuwar sassan kasa da kasa, ta kuma rungumi matakan da za su wanzar da daidaito tsakanin kasashen duniya, tare da ingiza zaman lafiya da tsaron shiyya da ma a sauran matakai.   (Saminu)

Saminu