logo

HAUSA

Sin Da Rasha Sun Amince Su Ci Gaba Da Aiwatar Da Yarjejeniyar Hadin Gwiwar Makwabata Da Abokanta

2021-06-28 20:10:17 CRI

Sin Da Rasha Sun Amince Su Ci Gaba Da Aiwatar Da Yarjejeniyar Hadin Gwiwar Makwabata Da Abokanta_fororder_china

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin ta kafar bidiyo. Wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin suka fitar bayan ganawar, sun sanar da fadada yarjejeniyar alakar makwabtaka da abokanta mai kyau a hukumance.

Shugaba Xi ya bayyana cewa, hadin gwiwar kasashen biyu ta karfafa wa kasashen duniya gwiwa, a gabar da duniya ke fuskantar rashin tabbas da sauye-sauye da ma yadda ci gaban bil-Adam ke fuskantar matsaloli iri-iri.

Xi ya kara da cewa, kasashen biyu sun nuna kyakkyawan misali na sabon tsarin alakar kasa da kasa. Yana mai cewa, manufar karfafa yarjejeniyar hadin gwiwar makwabtaka da aboka mai kyau, ta dace da muhimman muradun kasashen biyu, da jigon da ake ciki na zaman lafiya da ci gaba, shi ne kuma tsarin gina sabon hadin gwiwar kasa da kasa da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. A don haka, kasashen Sin da Rasha za su ci gaba da hada kansu duk da matsalolin da za a iya fuskanta yayin cimma wannan buri.(Ibrahim)

Ibrahim