Kasar Sin tana fatan Amurka za ta waiwayi yanayin da ake ciki ta kuma guji aikata kuskuren da ta aikata a Afghanistan
2021-09-02 20:25:19 CRI
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana Alhamis din nan cewa, kalaman da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi game da matakan da Amurka ta dauka a kasar Afghanistan, abin dubawa ne, kuma kasar Sin tana fatan bangaren Amurka, zai koyi darasi ya kuma kaucewa maimaita kura-kuran da ya tafka a kasar Afghanistan.
Shugaba Putin ya bayyana a kwanakin baya cewa, manufar kasancewar sojojin Amurka a kasar Afghanistan na tsawon shekaru 20, ita ce gabatar ta dabi’u da ka’idojinta ga kasar Afghanistan daga dukkan fannoni, ciki har da sauya tsarin siyasar kasar, amma daga karshe ta haifar da mummunar hasara da bala’i ga al’ummomin Amurka da Afghanistan, inda ya bayar da misali da yanayin da ake ciki a halin a kasar Afghanistan. (Ibrahim)
Labarai Masu Nasaba
- Lokaci Ya Yi Da Amurka Ta Kawo Karshen Hayaniyar Siyasa Kan Gano Asalin Kwayar Cutar COVID-19
- Shugaban Iran ya soki Amurka da lalata zaman lafiya a duniya
- Kasar Sin Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Kiyashin Da Amurka Ta Yi Wa ‘Yan Afghanistan
- Abun Da Amurka Take Yi, Mumuman Cikas Ne Ga Yaki Da Annoba Da Gano Asalin Kwayar Cuta A Duniya