logo

HAUSA

Xi ya yi jawabi a taron kolin CELAC

2021-09-19 16:36:09 CRI

图片默认标题_fororder_1127879678_16319922145701n

Jiya Asabar ranar 18 ga wata an gudanar da taron kolin shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashe mambobin kungiyar kawancen kasashen Latin Amurka da yankin Caribbean CELAC karo na 6, a birnin Mexico, hedkwatar kasar Mexico. Bisa goron gayyatar da kasar Mexico ta yi masa, wacce ke jan ragamar shugabancin CELAC, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a taron kolin.

Shugaba Xi ya ce, kasar Sin tana dora muhimmanci matuka wajen karfafa huldarta da CELAC, da kuma goyon bayan kungiyar ta CELAC wajen jagorantar kasashen shiyyar don yin hadin gwiwa tare da daidaita kalubaloli.

Ya kara da cewa, tun a shekarar bara, yayin fama da annobar COVID-19 wacce ta barke ba zato ba tsammani, Sin da kasashen Latin Amurka sun tallafawa juna kana sun yi hadin gwiwa da junansu daga dukkan fannoni domin yaki da annobar.

Shugaba Xi ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da tallafi ga kasashen Latin Amurka da yankin Caribbean gwargwadon karfinta, kana za ta taimakawa kasashen dake shiyyar domin samun nasarar kawo karshen annobar a kan lokaci da samun farfadowar harkokin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’ummar kasa. Shugaban kasar Sin ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Latin Amurka da yankin Caribbean domin haye wahalhalu tare, da kuma yin hadin gwiwa don samar da damammakin gina makomar al’umma ta bai daya tsakanin Sin da Latin Amurka.(Ahmad)

Ahmad