logo

HAUSA

Xi Ya Halarci Bikin Bude Taron Dandalin Tattalin Arzikin Gabashi Karo Na 6

2021-09-03 20:34:35 CRI

Xi Ya Halarci Bikin Bude Taron Dandalin Tattalin Arzikin Gabashi Karo Na 6_fororder_x

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bikin bude zaman taron dandalin tattalin arziki na gabashi karo na 6 ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi daga nan birnin Beijing.

Yayin jawabin Xi, ya yi kira ga dukkan bangarorin dake yankin arewa maso gabashin Asiya, da su hada hannu wajen magance mawuyacin halin da ake ciki tare da tsara wani shiri na samun ci gaba tare.

Xi ya ce, yau ne aka cika shekaru 76 da al’ummar Sinawa suka yi nasara kan mamayar maharan Japanawa da yaki da masu nuna danniya a duniya. Yana mai cewa, wajibi ne kasa da kasa su kare sakamakon babban yakin duniya na biyu, su kuma kare gaskiya na tarihi su himmatu wajen amfani da tarihi a matsayin wani madubi, da zai shata makoma mai haske a nan gaba.

Ya kara da cewa, yanzu hadin gwiwar da ake yi a shiyyar arewa maso gabashin yankin Asiya tana fuskantar wasu kalubaloli da muhimman damammaki. Yana mai cewa, ya dace dukkan bangarori su shiga a dama da su cikin abubuwan dake faruwa a yankin, yayin da suke sabawa da yanayin da duniya ke ciki, su hada hannu wajen magance mawuyacin halin da ake ciki, su kuma fito da wani shiri na samun ci gaba tare.

Shugaban kasar Sin ya ce, akwai bukatar mu taimakawa juna, don magance kalubalen da annobar COVID-19 ta haifar, yana mai kira da a kara kaimi a hadin gwiwar bincike da samar da alluran riga kafi, da kara samar da alluran a matsayin hajar da kowa zai yi amfani da ita a duniya, da yin watsi da siyasantar da alluran riga kafin COVID-19, da ma aikin binciken gano asalin kwayar cutar, da gina al’umma mai makomar bai daya a fannin kiwon lafiya.

Ya kuma yi kira ga dukkan sassa da su kara zage damtse, wajen ciyar da hadin gwiwar moriyar juna gaba, da zurfafa hadin gwiwa tsakanin shawarar “ziri daya da hanya daya” da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Turai da Asiya, da goyon bayan raya tattalin arzikin zamani, da hada hannu don tunkarar matsalar sauyin yanayi, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma a yankin.(Ibrahim)

Ibrahim