logo

HAUSA

Shugabannin Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

2021-09-10 11:57:59 CRI

Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, sun tattauna ba tare da wata rufa-rufa ba kan wasu batutuwa ta wayar tarho, bisa gayyatar da aka yi masa.

A cikin tattaunawar, Xi Jinping ya ce, a baya manufofin Amurka kan kasar Sin sun kawo cikas wajen raya hulda tsakanin kasashen biyu, lamarin da bai dace da babbar moriyar jama’arsu da kuma muradun bai daya na kasashen duniya ba.

Xi ya jaddada cewa, yanzu kasashen duniya na fuskantar wasu matsaloli tare, kamata ya yi Sin da Amurka su yi hangen nesa, su sauke nauyin dake wuyansu, su rika neman samun ci gaba, su nuna jarunta ta fuskar siyasa bisa manyan tsare-tsare, a kokarin mayar da huldar da ke tsakaninsu kan hanyar da ta dace cikin hanzari, ta yadda za a kara kawo wa jama’ar kasashen 2 da al’ummomin kasa da kasa fatan alheri.

A nasa bangaren, Biden ya ce, Amurka ba za ta sauya manufar “kasar Sin daya tak a duniya” ba. Kuma tana son kara mu’amala da tattaunawa da kasar Sin cikin sahihanci, su kuma tabbatar da muhimman fannonin da bangarorin 2 suka mai da hankali a kai da kuma sanya su gaban komai domin hadin gwiwa, su kuma kaucewa rashin fahimtar juna da rikicin ba-zata a tsakaninsu, a kokarin farfado da huldar da ke tsakaninsu yadda ya kamata.  (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan