logo

HAUSA

Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Baje Kolin CIFTIS Na Shekarar 2021 Ta Kafar Bidiyo

2021-09-02 21:03:41 CRI

图片默认标题_fororder_x

A yau ne aka bude bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2021 (CIFTIS) a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Cikin jawabin nasa, Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi aiki tare da sauran sassan duniya, don kara bude kofofinta ga ketare, da yin hadin gwiwa da cin moriyar juna da samun nasara tare, da raba damammaki wajen raya cinikayyar hidimomi, da yayata farfado da tattalin arzikin duniya da samun bunkasuwa.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta kara bude kofofinta, ta hanyar aiwatar da matakan rage sassan da a baya aka haramta cinikayya tsakanin kasashe a duk fadin sassan kasar, da kafa yankunan kirkire-kirkiren cinikayyar hidimomi na gwaji. Haka kuma kasar Sin za ta fito da karin damamamaki na hadin gwiwa, ta hanyar kara taimakawa ci gaban bangaren samar da hidimomi a kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya”, da raba nasarorin da kasar Sin ta cimma a fannin kimiyya da sauran kasashen duniya.

Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta kara inganta dokokin da suka shafi bangaren samar da hidimomi, ta hanyar taimakawa sashen da ma sauran yankuna, wajen gwada hade dokoki na cikin gida da wadanda ake amfani da su a yarjejeniyoyin cinikayya maras shinge na kasa da kasa, da kafa yankunan cinikayya na zamani na gwaji. Ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan raya shirin raya kirkire-kirkiren kanana da matsakaitan masana’antu da kafa kasuwar hannayen jari ta Beijing a matsayin dandalin farko da zai taimaka ga kananan da matsakaitan masana’antu.

Sama da kamfanoni 10,000 daga kasashe da yankunan 153 ne suke halartar bikin na wannan shekara, wanda aka gudanar a nan birnin Beijing, daga yau 2 zuwa 7 ga watan Satumba, bisa taken “Zuwa ga makomar fasahar zamani yayin da hidimomi ke kara azama kan ci gaba”.(Ibrahim)

Ibrahim