logo

HAUSA

Matasan Kenya sun nuna kwarewa a gasar wasan Kungfu

2021-06-14 15:53:10 CMG

Matasan Kenya sun nuna kwarewa a gasar wasan Kungfu_fororder_kenya

A jiya ne, matasan kasar Kenya suka nuna kwarewarsu a gasar fasahar wasan Kungfu, yayin da kulob-kulob guda 8 suka fafatawa a gasar Kenya Open Kungfu Wushu irinta ta farko, da aka shirya a garin Kiambu dake wajen Nairobi, babban birnin kasar.

A jawabinsa shugaban kungiyar wasan Kungfu na kasar Kenya, Ngaruiya Njonge ya bayyana cewa, wasan ya bunkasa tun a shekara 2016 saboda warzuwar al’adun kasar Sin a kasar Kenya. Wasan Kungfu a matsayinsa na wani bangane na al’adun Sinawa, yana kara farin jini a kasar Kenya.

Babban jami’in kula da harkokin al’adu a ofishin jakadancin kasar Sin dake Kenya Zhou Meifen, ya ce muhimmancin al’adu game da fasaha, zai taimaka wajen hada jama’ar Kenya da na kasar Sin waje guda. Kuma ofishin jakadancin Sin dake Kenya, ya taimaka wajen shirya gasar ta yini guda, a wani bangare na kokarin kara fahimta tsakanin al’ummomin kasashen biyu.

A cewar Jude Njomo, wani dan majalisar yankin, wasan Kungfu yana kara samun gindin zama a matsayin wasa, musamman tsakanin yara ‘yan makaranta.

Njomo ya ce, karin makarantu za su fara shigar da wasan, saboda irin rawar da yake takawa wajen bunkasa alaka tsakanin Sin da Kenya. Baya ga yaren Sinanci, za kuma a koyar da fasahar wasan na Kungfu a makarantu.(Ibrahim Yaya)

Ibrahim