logo

HAUSA

Kenya ta yi bikin ranar ma’aikata ta duniya cikin yanayin radadin annoba

2021-05-02 16:02:08 CRI

Kenya ta yi bikin ranar ma’aikata ta duniya cikin yanayin radadin annoba_fororder_0502-kenya

Rashin biyan kudaden albashi, sauye-sauye, yanke kudaden albashi, yawan ma’aikatan da ba su tabuka komai, da kuma yin aiki daga gida, na daga cikin kalaman da ake yawan furtawa a tsakanin ma’aikatan kasar Kenya, yayin da suka bi sahun takwarorinsu a sassan duniya wajen gudanar da bikin ranar ma’aikata ta kasa da kasa a ranar Asabar.

Ko da yake, kalaman dake shafar ‘yan kwadago an sha nanata su a Kenya shekaru da dama da suka shude, annobar COVID-19 ta jefa wasu ma’aikatan da dama cikin yanayin rashin tabbas a kasar ta gabashin Afrika.

Tun bayan barkewar annobar COVID-19 a Kenya a watan Maris na shekarar 2020, ma’aikata da dama sun rasa ayyukansu yayin da wasu aka dena biyansu kudaden albashi ko kuma ake zaftare masu kudaden da  suka zarta kashi 60 bisa 100 na albashinsu.

Alkaluman baya bayan nan da hukumar kididdigar kasar Kenya ta fitar sun bayyana adadin mutanen da suka rasa ayyukansu a kasar a sanadiyyar annobar ya kai kusan miliyan biyu.

Annobar ta jefa fannin kwadagon kasar Kenya cikin rudani, yayin da a hannu guda ta tilastawa wasu hukumomi daukar matakai daban daban kamar zaftare albashin ma’aikatansu domin kaucewa sallamar ma’aikatan daga bakin aiki, yayin da ma’aiktan ke cigaba da kai zuciyarsu nesa sakamakon tsananin rashin aikin yi da ake fama da shi.(Ahmad)

Ahmad