logo

HAUSA

Kenya ta kaddamar da bikin giwaye don bunkasa kare gandun dabbobi

2021-06-15 10:18:45 CRI

Kenya ta kaddamar da bikin giwaye don bunkasa kare gandun dabbobi_fororder_大象

A jiya Litinin kasar Kenya ta kaddamar da wani gagarumin bikin giwaye da nufin kare halittun dabbobin daji.

Najib Balala, babban sakatare a ma’aikatar yawon bude ido da kula da gandun daji na kasar, ya ce bikin wanda za a dinga gudanarwa a duk shekara a ranar 12 ga watan Agusta, a matsayin ranar giwaye ta duniya, za a dinga yin gangamin wayar da kai game da matsalolin da giwaye ke fuskanta da kuma yin gangamin tabbatar da kare gandun dabbobi.

Shirin zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa matakan da ake bi wajen kare dabbobi bai fuskanci wasu matsaloli ba kamar annobar COVID-19, a cewar Balala, wanda ya bayyana hakan a lambun shakatawa na kasa na Amboseli, mai nisan kilomita 240 daga Nairobi babban birnin kasar.

A cewar ma’aikatar yawon bude ido ta kasar, Kenya tana da giwaye sama da 34,000, kuma adadinsu yana karuwa sannu a hankali a duk shekara da kashi 2.8 bisa 100 a cikin shekaru 30 da suka gabata.(Ahmad)