logo

HAUSA

Xi Jinping: Kasashen BRICS sun zama wani muhimmin karfi a fagen harkokin kasa da kasa

2021-09-09 20:57:21 CRI

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS karo na 13 ta kafar bidiyo, inda ya bayyana cewa, bana ne ake cika shekaru 15 da kulla hadin gwiwar kungiyar kasashen BRICS. Xi ya ce shaidu sun tabbatar da cewa, duk matsalolin da muka shiga, muddin muka yi tsaya waje guda muka kuma yi aiki tare, hadin gwiwar BRICS zai ci gaba yadda ya kamata. A shekarar badi ne, kasar Sin za ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar kasashen na BRICS, da ma karbar bakuncin taron shugabannin kasashen kungiyar karo na 14.(Ibrahim)