logo

HAUSA

Xi Jinping: ya kamata a bi ra’ayin bangarori daban daban da sada zumunta da hadin gwiwa don samun moriyar juna

2021-09-04 20:12:20 CRI

Xi Jinping: ya kamata a bi ra’ayin bangarori daban daban da sada zumunta da hadin gwiwa don samun moriyar juna_fororder_0904-1

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bikin bude zaman taron dandalin raya tattalin arzikin gabashin Asiya karo na 6 ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi daga nan birnin Beijing.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana samun gagagrumin canji a duniya, inda ake fuskantar cutar COVID-19, da kokarin farfado da tattalin arzikin duniya. Kana a yankin gabashi da arewacin nahiyar Asiya kuma, ana fuskantar gagarumar dama tare da kalubale yayin da ake hadin gwiwa da juna. Don haka, ya kamata bangarori daban-daban su yi la’akari da yanayin yankin, da duba duniya baki daya, don warware matsaloli da samun ci gaba tare.

Ya ce a bana aka cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma Sin ta riga ta bude sabon babi na zamanintar da kanta bisa tsarin gurguzu a dukkan fannoni. Ya ce Sin tana son hada hannu da bangarori daban-daban, da bin ra’ayin bangarori daban-daban da sada zumunta da hadin gwiwa, don samun moriyar juna, yana mai cewa ta hakan, za a sa kaimi ga cimma burin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’Adama yadda ya kamata. (Zainab)