logo

HAUSA

Shugaban Amurka ya ba da umarnin bayyanawa jama’a wasu daga cikin bayanan harin ranar 9/11

2021-09-04 17:11:05 CRI

Shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya umarci hukumomin gwamnatinsa da su sake nazari tare da sakin wasu takardun dake da alaka da binciken da hukumar leken asiri ta FBI ta yi, kan hare-haren ta’addanci da suka auku a kasar a ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001.

Umarnin ya nemi ma’aikatar shari’a da sauran hukumomin gwamnatin, su sake nazarin takardun sannan su fitar da wasu bayanan da a baya suke matsayin na sirri, cikin watanni 6 masu zuwa.

Biden bayyana cikin wata sanarwa cewa, bai kamata a manta da juriyar iyalai da ‘yan uwan mutane 2,977 da suka mutu yayin harin mafi muni a tarihin Amurka ba.

Shugaban kwamitin leken asiri na majalisar wakilan kasar Adam Schiff, ya ce an kafa wani kwamitin da zai sa ido kan aikin nazarin, domin tabbatar da dukkan hukumomi sun kiyaye umarnin shugaban na tabbatar gaskiya, yayin da suke aikin.

Wasu daga cikin iyalan wadanda harin ya rutsa da su, sun shafe shekaru da dama suna neman gwamnatin ta saki wasu bayanan da za su yi wa jama’a karin haske dangane da lamarin. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha