logo

HAUSA

Amurka za ta daina aikin yaki a Iraq zuwa karshen bana

2021-07-27 11:17:19 CRI

Shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana cewa, sojojin kasarsa za su kawo karshen aikinsu na yaki a Iraq zuwa karshen bana.

Joe Biden ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake ganawa da Firaministan Iraq Mustafa al-Kadhimi dake ziyara a Amurkar.

Shugaban ya ce aikinsu a Iraq shi ne ci gaba da bayar da horo da taimako, da taimakawa wajen tunkarar kungiyar IS idan akwai bukata, amma zuwa karshen bana, Amurka ba za ta shiga aikin yake-yake ba.

Yanzu haka akwai kimanin dakarun Amurka 2500 a Iraq. An tura dakarun kawance da Amurka ke jagoranta zuwa Iraq ne, domin taimakawa dakarun kasar a yaki da kungiyar IS da horar da su tare da ba su shawara. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha