logo

HAUSA

Biden: Akwai yiwuwar kai harin ta’addanci a filin jirgin saman Kabul nan da sa’o’i 36

2021-08-29 16:40:54 CRI

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi gargadi a ranar Asabar cewa, akwai yiwuwar a sake kaddamar da harin ta’addanci a filin jirgin saman Kabul nan da wasu sa’o’i 24 zuwa 36 masu zuwa.

Mista Biden ya bayyana haka cikin wata sanarwa bayan kammala ganawa da tawagar jami’an kula da harkokin tsaron Amurka. Ya kara da cewa, halin da ake ciki a yanzu yana ci gaba da kasancewa mai matukar hadari, kuma akwai mummunar barazanar yiwuwar fuskantar hare-haren ta’addanci a filin jirgin saman.

Shugaban ya ce, ya umarci jami’an tsaron su dauki dukkan matakan da suka dace domin ba da kariya, kuma su tabbatar su yi amfani da dukkan matakan tsaro da dabaru don kare dukkan Amurkawa maza da mata dake kasar a halin yanzu.

An kashe dakarun tsaron Amurka 13 da wasu fararen hular kasar Afghanistan kimanin 170 a harin kunar bakin wake da aka kaddamar a wajen filin jirgin saman Kabul a ranar Alhamis. Kungiyar ISIS-K, wata kungiya a kasar mai alaka da kungiyar IS a Afghanistan, ta dauki alhakin kaddamar da harin.

Domin mayar da martani kan kazamin harin, a ranar Juma’a sojojin Amurka sun kaddamar da hari ta jirgin sama marar matuki kan kungiyar ‘yan ta’addan a lardin Nangarhar dake gabashin kasar Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mambobi biyu na kungiyar da kuma raunata wani guda, kamar yadda ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana.(Ahmad)

Ahmad